12.2 C
Ottawa
11.7 C
Manchester
Friday, September 17, 2021

Latest Posts

Facundo Pellistri: zai buga wa Alaves wasannin aro daga Manchester United

Man United sun ara Facundo Pellistri ga Alaves a Sifaniya

Matashin dan kwallon Manchester United, Facundo Pellistri ya koma Alaves, domin buga mata wasannin aro don fuskantar kakar 2021/22.

Alaves wadda ke buga gasar La Ligar Sifaniya ce ta sanar da haka a ranar Alhamis.

Mai shekara 19, bai buga wa United babban wasa ba, tun bayan da ya koma Old Trafford daga Penarol ta Uruguay.

United ta sayi dan kwallon a cikin watan Oktoban 2020 kan fam miliyan tara.

Pellistri ya yi wa Alaves wasannin aro 12, bayan da ya koma Sifaniya a zagaye na biyu a gasar, inda kungiyar ta kammala kakar da ta wuce a mataki na 16 a kasan teburi.

Latest Posts

spot_img

Don't Miss